Tinubu ya bada umarnin dakatar da shirin N-Power da sauran shirrye-shiryen tallafawa marasa karfi

0 163

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi umarnin dakatar da ilahirin shirrye-shiryen tallafawa marasa karfi da ke karkashin kulawar hukumar ayyukan jinkai da yaki da fatara, matakin da ke zuwa bayan zargin badakalar rashawar da ta dabaibaye ma’aikatar.

Wata sanarwa da Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fitar a yammacin jiya juma’a mai dauke da sa hannun kakakin ofishin Segun Imohiosen ta ce shugaba Tinubu ya yi umarnin dakatar da shirye-shiryen nan take.

A cewar sanarwar shirye-shiryen da dakatarwar ta shafa sun kunshi N-Power da Conditional Cash Transfer sai shirin bayar da jari da kuma ciyar da daliban Firamare da gwamnatin Najeriyar ta shafe shekaru ta na yi a sassan kasa.

Kamar yadda sanarwar ta ambata, dakatarwar za ta kasance ta wucin gadi zuwa nan da makwanni 6 don gudanar da bincike a hukumar dangane da badakar rashawar da ta dabaibayeta, gabanin duba yiwuwar dawo da su ko muma maye gurbinsu da wasu. A baya-bayan nan ne dai shugaban kasar Bola Tinubu ya dakatar da ministar ayyukan jinkai Betta Edu kan badakalar Naira miliyan 585 wadda tuni ta fara fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC

Leave a Reply

%d bloggers like this: