Ministan lafiya Ali Pate ya gargadi asibitocin kasar nan da su fifita ceton rayukan mutane fiye da kowane abu

0 192

Ministan kiwon lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya gargadi asibitocin kasar nan da su fifita ceton rayukan mutane fiye da kowane abu.

Bisa al’ada, sau da dama asibitoci basa karbar marasa lafiya sai an cika wasu ka’idoji, musamman raunin harbin bindiga, har sai an bayar da rahoton ‘yan sanda.

Sakamakon haka, lamarin dake kawo tsaiko wani lokaci ya kai ga galabaita ko rasa rayuwa.

Ministan lafiyan, wanda ya yi wannan gargadin a wata hira da manema labarai, ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da umarni ga asibitoci da su rika ceton rayuka da farko kafin fara wasu bukatu.

Farfesan ya ce ana sa ran jihohi a fadin kasar ma za su bi umarnin gwamnatin tarayya a asibitocin su daban-daban, yana mai jaddada cewa asibitoci masu zaman kansu su ma suna da hakkin bin wannan umarnin.

Ya tunatar da su cewa a matsayinsu na ma’aikatan lafiya, ceton rayuka shi ne matakin farko kafin komai a duniya, yana mai jaddada cewa Nijeriya ba za ta iya bambanta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: