Mutane 145 ne suka mutu yayin wasu hare-hare a jihar Filato

0 177

Akalla mutane 145 ne suka mutu yayin da aka kai wasu hare-hare cikin kauyuka 23 dake jihar Filato.

Maharan sun kashe mutane 113 cikin kauyuka 20 dake karamar hukumar Bokkos yayin da aka halaka mutane 32 cikin kayuka uku a karamar hukumar Barikin Ladi.

Rahotanni sun bayyana cewa, maharani sun kai hare haren ne daga dadaren  ranar asabar  zuwa safiyar jiya litinin.

Wannan hare-haren sun jikkata mutane da dama yayin da aka samu asarar dumbin dukiya.

Wuraren da harin ya shafa sun hada da Ruku da Hurum da Darwat da Mai Yanga Sabo da kuma kauyan NTV dukkanin su a gundumar Ropp. Shugaban kwamittin shiga tsakani kan rikici a yankin Monday Kassah ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a jiya litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: