Gwamnati na baza ta dena aiki tukuru ba wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan

0 198

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yace gwamnatin sa baza ta dena aiki tukuru ba, wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan da samar da damar-maki ga matasa, domin damawa da su a fannonin kasuwanci dana tattalin arziki.

Shugaba Tinubu ya fadi haka ne jiya a gidan sa dake Legas, yayin ganawa da shugabannin gargajiya dana kananan hukumomi da shugabannin cigaban al’umma, ‘Yan siyasa da masu rike da ofisoshin gwamnati.

A cewar shugaban kasar,yanzu haka ana kan hanyoyin samar da cigaban kudade da gyara masana’antu karkashin shirin gwamnatin sa na kyakkaywan fata. Ya bukaci ‘Yan kasa su kasance masu hakuri da bada goyan baya dangane da gyare-gyaren da ake gudanarwa a kasar nan domin dawo da tattalin arzikin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: