Gwamnatin tarayya ta jajantawa iyalan wadanda harin Jihar Filato ya shafa

0 200

Gwamnatin tarayyar ta kuma bada umarnin bayar da kayan agaji domin ragewa mutanen yankunan radadin abinda ya same su.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Ministan yada labarai da wayar da kan Jama’a Mohammed Idrisya fitar jiya a Abuja.

Gwamnatin tarayya tayi Allah Wadai da mummunan harin da aka kai kwanan-nan kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi a Jihar Filato.

Mohammed Idris yace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar Jinkai da yaki da fatara da sauran hukumomin da lamarin ya shafa suyi aiki tare da gwamnatin Jihar domin isar da kayan agaji ga wadanda harin ya shafa.

Ministan yada labaran yace, gwamnatin tarayya ta nuna matukar damuwar ta bisa faruwar wannan lamari, inda tayi alkawarin yin aiki tare da gwamnatin jihar domin tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya. A cewar Ministan,a mataki na gwamnatin tarayya hukumomin tsaro da na leken asiri, sun hada hannu wuri guda a kokarin magance matsalar tashe-tashen hankula.

Leave a Reply

%d bloggers like this: