‘Yan Majalisu sun yi kira da a gaggauta gabatar da hujjoji kan kashe mutane sama da 150 a jihar Filato

0 171

‘Yan Majalisun wakilai na arewacin kasar sun yi kira da a gaggauta gabatar da hujjoji dangane da kashe mutane sama da 150 ranar jajibirin Kirisemeti a Jihar Filato.

Wannan kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ‘Yan majalisar wakilai na arewacin Najeriya Alhassan Ado Doguwa ya fitar a daren jiya.

‘Yan Majalisar wakilan na arewacin kasar nan sun yi Allah wadai da kisan,suna masu cewa dole a nemo wanda suka kai wannan hari domin su fuskanci hukunci.

Sanarwar ta kara da cewa, yanzu Jihar Filato ta kasance inda ake kai munanan hare-hare musamman a yankunan manoma. Kazalika, ‘Yan majalisar sun bayyana cewa sun samu labarin kiasan gillar da aka yiwa mutane a kauyuka 23 na kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi a ranar jajibirin Kirsimeti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: