Gwamna Namadi ya bada umarnin inganta gidajen rediyon dake fadin jihar Jigawa

0 196

Gwamnatin jihar Jigawa zata farfado tare da inganta tashar gidan Radion FM Andaza da kuma sauran tashoshin FM dake fadin jihar nan.

Babbar mataimakiya ta musamman ga gwamnan jihar Jigawa kan kafafan yada labarai , Hajia Zainab Shuaibu Rabo Ringim ta sanar da hakan ga manema labarai.

Tace tuni Gwamna Umar Namadi ya bada umarnin dubawa da kuma gabatar masa da bukatun tashoshin na FM  domin daukar matakan da suka dace.

Hajia Zainab Shuaibu Rabo Ringim ta kara da cewar , gwamnan ya kuma amince da shiryawa yan social media taron bitar sanin makamar aiki domin ilmantar da su hanyoyin aikewa da labarai ta kafar sadarwa ta zamani bisa tsarin doka.

Tace hakan zai basu damar kara lakantar hanyoyin zamani na tura aikace aikacen gwamnati kai tsaye zuwa kafofin sadarwa na zamani.

Hajia Zainab Shuaibu Rabo tana mai cewar gwamnati tana wani shiri na tura yan social media zuwa maaikatu da hukumomin gwamnati domin kara tallata aikace aikacen maaikatu da hukumomin gwamnati ta kafar sadarwa ta zamani domin duniya ta ga yadda gwamnatin jihar Jigawa ke gudanar da aiyukanta Ta bukaci hadin kai da goyan bayan kafafan yada labarai domin yayata kyawawan manufofin gwamna Umar Namadu guda 12.

Leave a Reply

%d bloggers like this: