Za’a bada guraben karo ilmi ga dalibai hamsin yan asalin jihar Jigawa

0 179

Shirin uwar gidan shugaban kasa mai suna Renewed hope Initiative, tare da hadin gwiwar wasu hukumomin bada tallafi na duniya zasu bada guraben karo ilmi ga dalibai hamsin yan asalin jihar Jigawa.

Sakataren zartarwa na Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Jigawa, Saidu Magaji ya sanar da hakan ga wakilinmu.

Yace shirin uwar gidan shugaban kasar sun bullo da tsarin bada guraben karo ilmi ne ga jihohin da suke da karancin samun Ilmi a kasar nan ciki harda jihar Jigawa.

Alhaji Saidu Magaji yace daliban da zasu cigajiyar shirin sun hadar da masu sakamakon jarabawar credit A biyar a sakamakon jarabawar NECO da WEAC.

Ya bukaci daliban jihar Jigawa da suke da shaawar samun guraben karatun dasu kai takardunsu zuwa hukumar bada tallafin karatu ta jihar Jigawa bayan bukukuwan kirsimeti Alhaji Saidu Magaji ya kara da cewar za a yi jarabawar gwaji domin zakulo wadanda suka cancanci yin karatu, inda za a baiwa kowane dalibi da ya samu nasarar dala dubu bakwai domin yin karatu a daya daga cikin makarantun dake karkashin makarantar koyan tattalin arziki ta afirka dake da rassa a sassan kasar nan.   Sai dai yace dalibin da ya rubuta jarabawar JAMB kuma ya sami maki 180 zai ci gajiyar shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: