Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar hada-hadar hannayen jari, ta shirya tsaf don fitar da naira daga duk wani dandamali na crypto a daidai lokacin da gwamnati ke kara kaimi wajen magance masu satar kudaden canji da masu satar dala.
Wannan ci gaban ya zo ne bayan wani yunkuri na baya-bayan nan da Gwamnatin Tarayya ta yi na daidaita kasuwar crypto ta da aka kiyasta dala biliyan 57.
Sabon Darakta-Janar na Hukumar, Emomotimi Agama, ya bayyana sabon shirin na gwamnati yayin ganawa da mambobin masana’antar blockchain a jiya Litinin.
Ya ci gaba da cewa hukumar da ke karkashin sa na shirin samar da sabuwar tsarin kadarorin dijital wanda zai ci gaba da dorewar Najeriya a matsayin cibiyar samar da kadarorin dijital na Afirka tare da mafita iri-iri.