Na tabbatarwa da shugaba Buhari babban kudirina na tsayawa takarar shugaban kasa —Tinubu

0 119

Asiwaju Bola Tinubu, jagora a jam’iyyar APC mai mulkin kasar, ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari kudirinsa na neman takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023 da ke tafe.

Tinubu ya bayan na hakan ne yayin ganawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja, babban birnin kasa.

A yau Litinin ce Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu, wanda da isarsa suka shiga ganawar sirri.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da jan kafar da ake yi ba wajen tsayar da ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC, wanda a nan ne za ta zabi shugabanninta.

Tun gabanin yanzu ta bayyana cewa Tinubu na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da ke hankoron samun tikitin takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben kasar na 2023.

A Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato, ya ganawa da Shugaba Buhari a kan batun babban taron jam’iyyar.

Jim kadan bayan ganawar ta su ce kuma Shugaban Kwamitin Riko na jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mlaa Buni na Jihar Yobe, shi me ya gana da shugaban kasar kan babban taron wanda shi jam’iyyar ta sanya gaba a halin yanzu.

Kazalika, a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan Talabijin na Kasa NTA, Shugaba Buhari ya gargadi jam’iyyar a kan ta yi taka tsan-tsan wajen warware duk wasu matsalolinta don gudun kada wata jam’iyyar adawa ta yi mata mahangurbar kwace madafan iko a zaben 2023.

Da dama dai daga cikin ’ya’yan jam’iyyar ta APC na ci gaba da bayyana damuwa kan makomar jam’iyyar, inda ake ta yi wa shugabanninta matsin lamba dangane da jan kafar da ake yi na fara shirye-shiryen babban taronta da ake sa ran gudanar da shi a watan Fabrairu.

Asalin Rahoton: Aminiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: