NLC da TUC reshen jihar Jigawa sun yi watsi da batun biyan karin albashin Naira dubu 10

0 137

Kungiyoyin Kwadago na kasa, NLC da TUC reshen jihar Jigawa sun yi watsi da batun biyan karin albashin Naira dubu 10 da gwamnatin jihar ta shirya fara biya daga watan jumairun daya gabata a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin man fetur.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan taron kungiyar kwadago ta jihar da aka gudanar jiya a Dutse babban birnin jiha.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabannin kungiyoyin NLC da TUC tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin ta bayyana sanarwar da gwamnatin jihar ta yi, na bayar da karin albashin ma’aikata a matsayin yarjejeniyar da ba a cimma matsaya ba.

Sanarwar ta ce, kwamitin tattaunawa na NLC kan karin albashi ya dade yana turawa jami’an gwamnatin batun tattaunawa kan karin albashin amma babu wata amsa.

Hadaddiyar kungiyar gwadagon ya bayyana mamakin ta kan kalaman kwamashinan yada labarai, cigaban matasa, wasanni da al’adu Sagir Musa kan kudurin gwamnati na biyan naira dubu 10 na tsawon watanni 3. Sai dai lokacin da aka tun tubi shugaban ma’aikatan jiha Muhammad K. Dagacire, yace kwamatin sasanton NLC yana da cikekkiyar masaniyan kan matakin da gwamnati ta dauka dangane da abinda ya shafi tallafin rage radadin cire tallafin man fetur ga ma’aikatan gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: