Al’ummar unguwar Mandara dake garin Hadejia sun shirya bikin karrama Dr. Usman Aliyu

0 304

Al’ummar unguwar Mandara dake karamar hakumar Hadejia sun shirya bikin karrama Dr. Usman Aliyu wanda ya kammala karatun digirin digir-gir a jami’ar Najeriya ta Nsuka.

Da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman shugaban karamar hakumar Hadejia Alhaji Abdulkadir Umar Bala T.O ya yabawa al’ummar unguwar bisa shirya kasaitaccen bikin karramawar domin godewa Allah SWT bisa zabar daya daga cikin su yayi masa ni’ima.

Ya hori al’ummar da su cigaba da karfafawa junan su guiwa, inda ya bayyana wannan a matsayin wani yunkuri na hadin kai da kaunar juna dake wanzuwa tsakanin mazauna unguwar.

Shugaban karamar hakumar wanda ya samu wakilcin sakataren karamar hakuma Alhaji Ahmed Hassan Yayari ya taya shi murnar kammala karatun digirin na digir-gir.

A jawabinsa shugaban taron Ambassador Haruna Ginsau Baraden Hadejia ya bukaci Dr. Usman daya kasance mai mutumin kirki a duk inda ya samu kansa. Tun da farko basaraken gargajiyar yankin, mai unguwar Mandara Alhaji Zubairu Alhassan yace sun shirya masa liyafar ne bisa kyawawan dabi’u da yake dasu, da kuma burinsa na cigaban al’ummar unguwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: