Najeriya ta yi gwaji ga sama da mutane 300,000 masu dauke da cutar tarin fuka

0 176

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce kasar Najeriya ta yi gwaji ga sama da mutane 300,000 masu dauke da cutar tarin fuka a shekarar 2023, wanda ya zama karo na farko a tarihi da aka samu adadi mai yawa kamar haka.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, a yayin taron hukumar karo na 37, wata kungiyar mai rajin tsayarda cutar tarin fuka ta gabatar da wani bayani game da yanayin cutar tarin fuka da kuma kokarin da suke yi na tabbatar da karuwar wasu karin kudade daga asusun duniya a kan magance cutar ta tarin fuka.

Najeriya, tare da sauran kasashe da da kuma mambobin kungiyoyin farar hula, sun bayyana ra’ayoyinsu da kuma ayyukansu, tare da bayyana abubuwan da suka samu daga Asusun Duniya.

Yayin da ya ke yabawa da ci gaban da aka samu, ya ce kasar na ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu kashi 100 bisa 100 na maganin cutar tare da kara yawan maganin rigakafin tarin fuka. Ya ce kasar nan ta kuma tanadar tsare-tsare da dabaru masu inganci don magance kalubalen da ake samu wajen neman hanyoyin kawo karshen cutar

Leave a Reply

%d bloggers like this: