NNPCL ya sanar da cewa za a rufe matatar Fatakwal don yin gyare-gyare

0 451

Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da cewa za a rufe matatar mai ta Fatakwal domin yin wasu gyare-gyare.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da NNPCL ya fitar a shafinsa na X, inda ya ce za a fara aikin daga yau Asabar, 24 ga Mayun 2025.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, don tabbatar da cewa aikin gyare-gyaren ya tafi yadda ake so da kuma bisa gaskiya,” in ji NNPCL.

Kamfanin ya ce a shirye yake a kowane lokaci wajen samar da isasshen makamashi a Najeriya.

Leave a Reply