Ma’aikatar Ilimin Firamare ta Jigawa ta gudanar da taron horo na rana guda ga Hadiman Gwamna kan Kula da Ilimi

0 438

Ma’aikatar Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa ta gudanar da taron horo na rana guda ga Hadiman Gwamna na Musamman kan Kula da Ilimi, da nufin inganta ayyukansu na sa ido da wayar da kai a makarantun jiha.

Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, wanda ya samu wakilcin Daraktan Horaswa da Daukar Ma’aikata, Alhaji Musa Ayuba, ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na ajandodon gwamnatin gwamna Umar Namadi 12 da nufin inganta koyarwa da koyo a matakin firamare.

Ya bayyana cewa horon ya mai da hankali ne kan rawar da Hadiman Gwamna za su taka wajen sa ido a makarantun gwamnati don tabbatar da cewa ana gudanar da darussa yadda ya kamata.

A yayin taron, kwararru da dama sun gabatar da takardu, ciki har da Daraktan Hukumar Tsare-tsaren Ilimi ta Firamare, Dr. Ya’u Ahmed Sara, mai ba Gwamna shawara kan Ilimi, Dr. Hauwa Mustapha Babura, da kuma Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Gumel, Malam Ibrahim Abdussalam, inda aka jinjina wa Gwamna kan daukar malamai sama da 3,000 da kuma amincewar sa da shirye-shiryen horar da ma’aikata a fadin jihar jigawa.

Leave a Reply