Munyi shirin kota kwana na gyaran hanyoyi da damina a jahar Jigawa – Shugaban Hukumar JIRMA

0 112

A yayinda daminar bana ke ƙara matsowa, hukumar gyaran hanyoyi ta jahar Jigawa tace ayanzu haka saura kaɗan ta kammala gyaran dukkanin hanyoyin da ambaliyar ruwan bara ta lalata su a sassan jahar daban-daban.

‎Shugaban hukumar Injiniya Abbas Muhammad Lalai ya sanar da hakan ga wakilin mu na Dutse Zulkiflu Abdullah Dagu a wata hira dayayi dashi a Ofishin sa dake Dutse.

‎Yace ko bayaga ƙoƙarin su na kammala waɗannan ayyuka, akwai tanadi na musamman da hukumar kedashi na shirin kota kwana a daminar bana na kula da kuma gyaran hanyoyin da ka iya samun matsala sanadin ambaliya wadda ba’a fatar hakan.

‎Dangane da ƙarancin kayan aiki da hukumar ke fuskanta, shugaban na JIRMA yace yanzu haka gwamnatin jahar ta ware  Naira miliyan ɗari domin sayen sabuwar matar Tifa baya ga gyaran tsaffin da suke da su.

Leave a Reply