Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauya tsarin tsaron Najeriya don bada tabbacin aikin ‘yan sandan jihohi da na cikin al’umma.

Jam’iyyar ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da ta yi Allah wadai da kisan uku daga cikin daliban da aka sace na jami’ar Greenfield ta Kaduna.

Sanarwar ta samu sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan.

A wani labarin kuma, Kungiyar Jama’ar Kudancin Kaduna a jiya ta yi zargin cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mutane akalla 65 yan kabilar Adara a karamar hukumar Kajuru da ke jihar.

Kungiyar ta ce daga cikin wadanda aka sace har da Hakimin Kauyen Libere, Bala Yero, da matansa, da wasu mutane 16.

Mai magana da yawun kungiyar, Luka Binniyat, a wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen da misalin karfe 11 na dare ranar Talata inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, tare da yin awon gaba da mutane.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: