Rahotanni daga garin Geidam a jihar Yobe sun ce ƴan bindiga da ake kyautata zaton mayaƙan ISWAP ne ko na Boko Haram sun yi mummunan ta’adi a yau Asabar bayan jami’an tsaro sun kore su a ranar Juma’a.

Mazauna garin sun ce mayaƙan sun fake a garin bayan Sojojin Najeriya da taimakon jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin saman kasar, sun kore su.

Bayanai sun ce mayaƙan sun kwashi abinci tare da cinna wa gidaje wuta.

Wani mazauni garin ya ce sun fake garin har sai da suka gyara motar da suka kwashi abinci bayan ta lalace.

Tun da farko kakakin ƴan sandan jihar Yobe ya ce mayaƙan sun watsar da wata takarda mai ƙunshi da kira ga mutane su ba su haɗin kai don su ƙwace garin su kafa daularsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: