Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na aiwatar da shirye-shirye masu kyau ga yanayi

0 99

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na aiwatar da shirye-shirye masu kyau ga yanayi kuma tana bin hanyar dorewa.

Ya yi wannan bayanin ne a wajen taron shugabanni kan yanayi wanda Shugaban Amurka, Joe Biden, ya hada, wanda aka gudanar daga ranar Alhamis zuwa Juma’a.

Yayin da yake jawabi ga shugabannin duniya kan kokarin da Najeriya ke yi kan sauyin yanayi ya zuwa yanzu, shugaban kasar ya ce tun bayan amincewa da yarjejeniyar Paris a shekarar 2016, Najeriya ta fitar da kudirori dayawa kamar su tsarin rage fitar da hayaki da kashi 20 cikin dari ba tare da wani sharadi ba da kuma kashi 45 bisa sharadi tare da goyon bayan kasashen duniya nan da shekarar 2030.

A bangaren samar da amfanin gona da samar da kayan noma, Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na kokarin habaka samar da amfanin gona ta hanyar ingantaccen hasashen yanayi ga manoma, da sauransu.

Ya karkare da kira ga sauya duniya zuwa tattalin arzikin bai daya gami da samar da cigaba mai dorewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: