Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta sha alwashin tsayar da komai cak a Najeriya muddin Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya aiwatar da aniyarsa ta korar ma’aikatan gwamnati a jihar.

Kungiyar kwadagon tace da farko za ta tafi yajin aikin gargadi na kwanaki 5, daga baya ya koma na sai baba ta gani matukar hukumomin da abin ya shafa suka kasa shawo kan El-Rufai akan ya watsar da shirinsa.

Gwamna Nasir El-Rufai yace gwamnatin jihar baza ta iya cigaba da daukar dawainiyar dumbin ma’aikatan gwamnatin da basa tsinana komai ba, bisa la’akari da raguwar kudaden shiga sanadiyyar karancin kudaden da ake samu daga tarayya, wanda annobar corona ta haifar.

Gwamnan na jihar Kaduna yace rage yawan ma’aikatan jihar daya ne daga cikin matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar karacin kudade.

Shugaban kungiyar ta NLC, Ayuba Wabba, ya nanata matsayar kungiyar a wajen taron manema labarai a Abuja, bayan ganawar kwamitin ayyukan kungiyar na kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: