Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta yanke na tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar.
A wata sanarwa da ta fitar jiya Laraba da daddare bayan yanke hukuncin, mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta Debo Ologunagba, PDP ta ce ta yi nazari kan hukuncin kuma ba ta yarda da shi ba dungurungum.
A jiya Laraba ne kotun ta yi zamanta na karshe don yanke hukunci a kan kararrakin da jam’iyyun PDP da na LP suka yi suna kalubalantar nasarar Bola Tinubu, inda aka shafe awa kusan 12 ana yanke hukuncin.
PDP ta ce a matsayinta na jam’iyya mai bin dokar kasa, tuni ita da lauyoyinta suka yi wa hukuncin kyakkyawan nazari tare da daukar mataki na gaba da ya dace bisa dokar shari’a.
Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta yi watsi da korafin Atiku Abubakar da ya nemi a soke sakamakon zaben shugaban kasa na jihohin Kano da Legas.
Kotun ta ce masu korafin ba su hada da Peter Obi da Rabiu Kwankwanso ba wadanda suka samu kuri’u mafi yawa a jihohin biyu.
Kotun ta kuma yi watsi da korafin Atiku Abubakar da na jam’iyyarsa ta PDP kan zargin cewa Shugaba Tinubu yana da takardar shaidar zama dan kasashe biyu da kuma na zargin tuhumarsa da safarar kwaya.