Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya ba da chekin Naira biliyan biyu ga kungiyar kwadago ta kasa (NLC), domin raba wa ma’aikatan jihar a matsayin rance mara ruwa mai wa’adin watanni 24 domin rage musu radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan ya bukaci kungiyar a ziyarar da ta kai masa ne ranar Talata da ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu cewa ta kammala tattaunawa da ma’aikatar kudin jihar domin tantance ma’aikatan da za su amfana da kuma yadda za a karbo rancen ta hanyar cirewa duk wata daga albashinsu.Ya kuma sanar da ninka kudaden biyan hakkokin tsoffin ma’aikata da suka yi ritaya na wata-wata inda ya umurci ma’aikatar kudi ta tantance ma’aikatan da ke bin kudadensu na sallama domin biyan su.
Wadanda za su amfana su ne wadadanda ba a biya su ba bayan sun ritaya daga 2016 zuwa 2018 bayan an tantance su a shekarar 2019.
Zulum ya ba da umarnin a biya ma’aikatan da ke bin bashin 2019 da 2020, wadanda suke daga 2021 zuwa yau za a biya su ne bayan kammala tantance su nan gaba.
Shekaru da dama aka kasa biyan tsoffin ma’aikatan Jihar Borno da suka yi ritaya kudaden su na sallama, wanda da zuwan Gwamna Zulum a zangon sa na farko ya fitar da kimanin Naira biliyan 20 domin rage bashin da suke bi a duk shekara.
A ganawarsa da NLC, Zulum ya sanar da raba motocin bas guda 30 na jigilar ma’aikata kyauta a Maiduguri zuwa wuraren aikinsu da zimmar rage musu radadin cire tallafin mai.
Hukumar Sufuri ta Borno Express ce za ta kula da motocin, wadanda za a tura su wuraren daukar mutane a manyan tituna da safe zuwa sakatariyar Musa Usman sannan a dawo da su da yamma.