PSG na zawarcin Rashford, Luis Diaz da B. Silver, Bayern Munich ta sabunta kwantiragin Alphonso Davie

0 240

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain PSG sun shiga zawarcin dan wasan Manchester United dan asalin kasar Ingila, Marcus Rashford. Kungiyar tayi wa dan wasan tayin albashin da ya kai £500,000 a kowanne mako.

A kokarin kara karfin gaban kungiyar ta PSG, kungiyar tana duba yiwuwar daukan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dan asalin kasar Columbia, Luis Diaz.

Kazalika, dan wasa Bernado Silver na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dan asalin kasar portugal na cikin komar ta PSG. Kungiyar za tayi amfani da dan wasa Xavi Simons ne a matsayin kakara wajen karbo dan wasan.

Bayern Munich ta sabunta kwantiragin dan wasan baya Alphonso Davies makon nan. Sun yi tayin biyansa albashin Yuro miliyan 14 a duk shekara domin kokarin hana shi komawa Real Madrid, amma wakilin Davies na bukatar Yuro miliyan 20.

Leave a Reply

%d bloggers like this: