Rikici ya ɓarke tsakanin ƴan majalisa a ƙasar Ghana kan ƙoƙarin gwamnati na fara karɓar haraji daga masu hada-hadar kuɗaɗe

0 248

Rikici ya barke tsakanin ‘yan majalisa a kasar Ghana kan kokarin gwamnati na fara karbar haraji daga masu hada-hadar kudade ta wayar salula da ake shirin kada kuri’a a kansa.

‘Yan majalisar dokokin na jam’iyyar NPP mai mulki da ta ‘yan adawa na jam’iyyar NDC sun bai wa hammata iska a lokacin da kakakin majalisa Joe Osei-Owusu ya tashi daga kujerarsa domin kada tasa kuri’ar ta amincewa da kudirin.

A lokacin ne ‘yan adawa suka yi yunkurin hana shi saboda majalisar ta sanar da su cewa shugaban majalisar ya zama dan ba-ruwanmu a mataki irin wannan.

Yayin da aka fara kada kuri’ar karkashin wani kudiri na gaggawa, ‘yan majalisa marasa rinjaye sun sha alwashin ba za su amince shugaban ya jefa kuri’arsa ba.

Jam’iyyar ta NDC mai adawa tace matakin karin harajin na kashi 1.75 cikin 100, zai kara matsin rayuwa ga marasa karfi a kasar.

Amma ministan kudi, Ken Ofori-Atta, yace matakin ya zama tilas domin fadada hanyoyin kudaden shigar gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: