Dakarun ƙasar Habasha sun sake ƙwato garin Lalibela mai tarihi daga hannun ƴan tawayen yankin Tigray

0 198

Dakarun kasar Habasha sun sake kwato garin Lalibela mai tarihi daga hannun ‘yan tawayen yankin Tigray.

Kungiyar ‘yan tawayen Tigray ta kasar ta ce ta yanke shawarar janye mayakanta daga dukkan yankunan lardunan Amhara da Afar.

Ta kara da cewa ta dauki matakin ne domin share fagen warware rikicinta da gwamnati cikin lumana.

Gwamnati ta sha kwato garin na Lalibela wanda ya sha komawa karkashin ikon ‘yan tawaye a lokuta da dama. An kuma lalata filin jirgin saman garin a fadan.

A ranar Asabar din da ta gabata gwamnatin kasar ta ce dakarunta sun sake kwace wasu garuruwa da dama ciki har da garin Weldiya.

Kungiyar ‘yan tawayen Tigray na ci gaba da janye mayakanta zuwa yankin da tafi karfi na Tigray bayan da aka tilasta mata yin watsi da shirinta na cigaba da kokarin kwace iko da Addis Ababa, babban birnin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: