Rikicin kabilanci na barazanar barkewa a yankin yammacin Darfur dake Sudan

0 223

Dubban mutane sun kauracewa yankin yammacin Darfur dake Sudan bisa barazanar barkewar rikicin kabilanci.

Shaidu sun kalubancin dakarun rundunar RSF da aka bayar da rahotan cewa sun kashe daruruwann fararen hula wadanda ba larabawa ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan rundunar ta RSF ta kwace iko da hedikwatar sojijin kasar dake yammacin El Geneina babban birnin Darfur.

Sai dai RSF tace bata da hannu a rikicin kabilancin dake faruwa a yankin. Kungiyoyin bayar da agaji a yankin sunce sama da mutane dubu 7 ne suka tsallaka zuwa Chadi cikin kwanaki 3 da suka gabata, wanda suka hada da mata da kananan yara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: