Risinawa a gaban majalisar ba ya nufin an tabbatar da wadanda aka tantance a matsayin ministoci

0 244

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shaida wa wadanda aka tantance matsayin ministoci cewa risinawa lokacin da suke gaban majalisar hakan ba ya nufin an wanke su ko kuma tabbatar da su a matsayin minista.

Akpabio ya yi wannan karin haske ne a lokacin da ake tantance wanda aka zaba daga jihar Anambra, Uju Kennedy-Ohanenye.

wadda ita ce mace ta farko da aka tantance a matsayin minista a ranar farko ta tantancewar, ita ce mace daya tilo da ta tsaya takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023. Ta kasance daya daga cikin mata bakwai da aka nada a jerin sunayen ministocin shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: