Bola Tinubu yayi alkawarin samar da motocin sufuri 3,000 ga matafiya a fadin Najeriya

0 366

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi alkawarin samar da motocin sufuri a dukkan jihohin Najeriya da kananan hukumomin a farashi mai sauki.

Shugaban kasar ya ce gwamantin sa zata samar da Naira Bilyan 100 daga yanzu zuwa watan Maris na shekara mai zuwa domin siyan motocin masu wuraran zama 20 dake amfani da gas wato CNG.

Shugaban kasar ya bayyana haka jiya a wani jawabi da yayi ga yan kasa, wannan wani mataki ne na rage radadin janye tallafin man fetur.

A cewar shugaba Tinubu, motocin na Bus za raba su ga manyan kamfanonin sufuri a jihohin Najeriya, kuma za suna tafiya mai nisa sosai.

Ya kuma kara da cewa gwamnati na aiki tare da kungiyoyin kwadago domin samar da karin albashi mafi karanci ga ma’aikata. Ya kuma yabawa kamfanoni masu zaman kan wanda tun farko suka karawa ma’aikatan su albashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: