Rundunar sojoji tayi nasarar kashe yan bindiga 7 cikin kwanaki uku a jihar Kaduna

0 160

Rundunar sojoji tayi nasarar kashe yan bindiga 7 a jihar Kaduna tsakanin ranakun laraba zuwa jiya juma’a.

Kakakin runduna ta 1, Lt.-Col Musa Yahaya ya bayyana haka jiya juma’a a Kaduna, cewa dakarun sojan suin kashe yan bindiga 4 a ranar laraba a karamar hakumar Birnin Gwari.

Yayi bayanin cewa, yayin samamen, rundunar ta gano bindiga kirar AK 4, da sauran makamai, da wayar hannu da babura 14 daga maboyar yan bindigar.

Ya kuma ce a ranar alhamis, wasu manoma dake girbin amfanin gona a yankin kauyen Sabon Sara saun kauracewa gonakin su saboda tsoron harin yan bindiga.

Ya kara da cewa, babban kwamandan runduna 1 na rundunar sojin Najeriya Maj.-Gen. Valentine Okoro ya jinjinawa dakarun bisa wannan nasara.

Okoro ya kuma yabawa manoman bisa kwarin guiwa da bayanai  da suka bayar. Ya hori dakarun da su cigaba da mamaye yan bindigar da sauran masu aikata laifuka domin tabbatar da dawo da tsaro a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: