Tinubu ya gode wa Faransa bisa yunkurin dawo da kudade kimanin $150M da Janar Abacha ya sace

0 173

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya godewa kasar Faransa bisa wani yunkuri na dawo da kudade kimanin dala miliyan 150 wanda tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha ya sace.

Shugaban kasar yayi kalaman godiyar ne a jiya Juma’a lokacin da ya karbi bakuncin ministar harkokin turai da kasashen wajen na Faransa Catherine Colonna, wanda kawo wata ziyara a madadin shugaban Faransa Emmanuel Macrona fadar shugaban kasa dake Abuja.

Tinubu ya yi maraba da yargegeniyar euro miliyan 100 tsakanin Najeriya da Faransa domin tallafawa shirin i-DICE, wani shirin gwamnatin tarayya na bunkasa harkokin zuba jari na fasahar sadarwar yanar gizo ICT, da kuma samar da masana’antun kirkira da kudan na Abacha.

Yarjejeniyar wacce ministan sadarwa da cigaban fasahar sadarwa Dr ‘Bosun Tijani da ministan harkokin turai da harkokin kasashen wajen Faransa suka sanyawa hannu a hedikwatar ma’aikatar harkokin wajen dake Gidan Tabawa Balewa.

Shugaban kasa wanda ya yaba da karfafar alakar deflomasiyya tsakanin kasashen biyu, yace wannan wani cigaba ne wanda ke zuwa bayan shiyarar shugaban kasa Faransa bayan rantsar dashi a matsayin shugaban kasa. Dangane da halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar Kuwa, Shugaban kasa Bola Tinub kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika yace Najeriya da duba yiyuwar warware rikicin siyasar kasar ta hanyar diflomasiyya domin kauracewa zubar da jinni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: