Tinubu ya hori ministocin sa da su ajiye muradun su a gefe su kyautata rayuwar yan Najeriya

0 162

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hori ministocin sa da su ajiye muradun su na kashin kai a gefe guda, tare mayar da hankali kan muradun gwamnatin sa na kyautata rayuwar yan Najeriya wajen magance talauci.

Yayi wannan gargadi jiya Juma’a a kashen taron kwanaki 3 da aka shiryawa ministoci, manyan sakatarori, da mataimakan shugaban kasa na musamman da sauran manyan mukarraban gwamnati a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Tinubu, wanda ya sanar da mahalarta taron cewa, nauyi a wuyan su, su sauya labarin kasar nan, inda yace idan suna da wata matsala da aikinsu, zasu iya tuntubar sa kai tsaye.

Ya kuma jaddada bukatar tabbatar da hadin guiwa wajen gudanar da ayyuka domin cimma burin bunkasa kasa. Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin tarayya ke bayyana shirin na ganowa tare war-ware matsaloli da kalubalen kasar nan, ciki har da majalisun kasa wanda har yanzu basu kammala aikin da aka basu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: