Shugaban kungiyar Hizbullah zai yi jawabi a karon farko tun bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas

0 360

A yau ne ake sa ran shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah zai gabatar da jawabi a karon farko a bainar jama’a tun bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas.

Ana bayyana damuwa kan watakil zai yi hannun ka mai sanda kan shigar Hezbollah yakin da ake yi a Gaza.

Tuni mayakan Hezbollah suka fara taho mu gama da sojojin Isra’ila a iyakar kasasashen biyu, ana kuma fargaba kan kungiyar ka iya zama wata jagaba a yakin.

A bangare guda Isra’ila ta gargadi Hezbolla, kan ta janye daga tsoma baki a yakin. Tun farkon harin baya-bayan nan da aka kai wa Isra’ila, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,400, Lebanon ta kasance a gefe, tana sa ido kan Hezbollah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: