Rundunar yan sanda ta jihar Jigawa ta kama mutum 2 bisa gagarumar sata a karamar hukumar Garki

0 136

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 2 bisa zargin su da Satar Sa a Karamar Hukumar Garki ta Jihar nan.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar nan ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Dutse.

A cewarsa, an kama mutanan ne bayan wani mai suna Nasiru Magaji ya kaiwa yan sanda rahotan shiga gidansa, tare da sace masa Saniya 1.

Sanarwar ta ce bayan samun rahotan ne yan sanda suka bi sawun barayin Saniyar da aka sace, inda kuma suka ganota a Kasuwar Wudil ta Jihar Kano.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce mutanen da aka kama din mazauna garin Jaya na Karamar hukumar Garki ne da kuma kyauyen Badage na Karamar hukumar Ringim, suna kuma cigaba da neman sauran barayin.

Kazalika, ya ce za’a gurfanar da mutanen a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da kamo sauran biyun da suka tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: