

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Kungiyar Fulani Makiyaya ta Kautal Hore a nan Jihar Jigawa ta ce ta kammala shirye-shiryen kafa sabuwar kasuwar Nona ta Zamani a nan karamar hukumar Hadejia.
Shugaban Kungiyar Alhaji Umar Dubantu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Dutse.
Alhaji Umar Dubantu, ya ce Kungiyar zata kafa sabuwar kasuwar ne da tallafin gwamnatin Jiha da kuma Karamar hukumar Hadejia.
Haka kuma ya ce Kungiyar ta share wurin da za’a kafa kasuwar domin ganin cewa aikin ya kankama cikin Nasara.
A cewarsa, bayan kammala ginin Kasuwar Fulani Mata zasu rika kawowa Nono daga garuruwan da suke Kasar Hadejia, ciki harda makotan Jihar Jigawa wanda suka hada da Katagum, Azare da kuma Nguru ta Jihar Yobe.
Haka kuma ya ce Kungiyar zata zabi Fulani 20 wanda zata bawa Na’urar Janareto ta hanyar bashi marar ruwa domin su rika Ajiye Nonan su.
Kazalika, ya ce Kasuwar zata samarwa Karamar Hukumar Kudin Shiga ta Fannin Rabanu.