

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
kimanin garuruwa 15 ne yan bindiga suka kaiwa hari a kusa da birnin Gusau na Jihar Zamfara tare da kashe mutane 7.
Mazauna garuruwan sun ce yan bindigar sun kai musu harin ne a ranakun Asabar da Lahadi.
Manema Labarai sun gano cewa baya ga kashe mutane, yan bindigar sun kuma sace Mata 33 wanda suka yi Garkuwa da su, kamar yadda mutanen da lamarin ya shafa suka fadawa BBC Hausa.
Daga cikin kyauyikan da yan bindigar suka kaiwa hari sun hada da Geba, Kura, Duma, Gana, Tsakuwa, Gidan Kada da Gidan Kaura.
A cewarsu, mafiya aka sari mutanen aka kaiwa garuruwan su hari sun tsere daga garuruwan inda suka samu mafaka a jerin gidajen gwamnati na Damba dake birnin Gusau.
Wani Mazaunin garin Gidan Kaura, yace daga cikin garuruwan da aka kaiwa harin ya tabbatar da mutuwar mutane 7, sai dai ya ce basu dauko gawar mutanen ba domin a yi musu Jana’iza.
Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai na Jihar Zamfara Malam Ibrahim Dosara, ya tabbatar da kaiwa harin, sai dai ya ce Jami’an tsaro sun kori yan Bindigar daga garuruwan.