Yadda wasu yan daba suka kai hari filin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taro a Jihar Zamfara

0 88

Rahotanni daga Jihar Zamfara na cewa wasu ‘yan daba sun kai hari filin da jam’iyyar PDP take gudanar da taro a babban birnin Jihar Gusau.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa tun da farko an so a gudanar da taron a Zaitun Oil mill, da ke bayan hukumar alhazai amma aka sauya zuwa Command Guest House da ke Gusau.

Rahotanni sun ce ‘yan dabar siyasa sun yi wa wurin dirar-mikiya da sanyin safiyar yau Litinin inda suka lalata kayayyakin zabe da foma-fomai da motocin ‘yan jam’iyyar PDP da kujeru, sannan suka cinna wuta kan rumfunan da aka kafa.

Hotunan da aka rika yadawa a safukan sada zumunta sun nuna yadda wurin ya kama da wuta bayan an yi kaca-kaca da shi.

Manema Labarai sun ambato Umar Aminu, wani hadimin mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, yana cewa babu wanda ya isa ya yi musu barazanar da za ta kai su fasa gudanar da taron.

An rawaito cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Barista Mahdi Aliyu Gusau da shugaban Jam’iyar PDP na rikon Kwarya a Jihar Ambassada Bala Mande, sun je wurin taron.

Taron ya gayyaci masu zabe a Jam’iyar su dubu 1,089 wanda sune zasu zabi Jagororin da zasu ja ragamar Jam’iyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: