Rushe-rushen da gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan kasuwa a filin Idi ya sanya asarar sama da N250Bn

0 296

Wata babbar kotun tarayya ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar naira biliyan 30 ga ƴan kasuwar da ta ruguza wa shaguna a Filin Babban masallacin Idi na Kano a watannin baya.

Mai shari’a S. A. Amobeda na babbar kotun tarayyar ne ya bayar da umarnin a wani hukunci da ya yanke yau Juma’a.

Waɗanda suka kai karar sun hada da ƴan kasuwa da masu shaguna da masu gidaje da ‘yan tebura a filin idin karkashin wata ƙungiya da ake kira Masallacin Idi Shop Owners Association

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da hukuncin har ma ta ce za ta daukaka ƙara.

Lauyan ƴan kausuwar Nuruddeen Ayagi ya ce kotun ta ce rushe-rushen da gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan kasuwa a filin Idin ya haddasa barnar da ta kai naira biliyan 250.

Ya kuma ce kotun ta hana gwamnatin jihar sayar wa wani filayen da ta rushe, ko a cikin Najeriya ko daga wajen Najeriya har abada.

Lauyan ya ƙara da cewa kotun ta kuma umarci gwamnatin kano ta mayarwa ‘yan kasuwar da ta rusawa shaguna, filayensu.

Sai dai lauyan gwamnatin jihar wanda kuma shi ne kwamishinan shari’a, Barister Haruna Deideri ya ce hukuncin babbar kotun tarayyar ba karbabbe ba ne.

Ya ƙara da cewa dokar mallakar ƙasa ta bai wa gwamna cikakken iko a kan ƙasa a ko ina take a cikin jihar da yake mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: