An gargadi gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara su daina aiyasantar da lamarin tsaro a jihar

0 145

Kungiyar shugabannin arewa da masu ruwa da tsaki a arewa ta gargadi gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara su daina aiyasantar da lamarin tsaro a jihar, da kuma wasa da ruyakan yan jihar, biyo bayan wata takaddama da aka samu a baya-bayan nan, inda gwamnatin jihar ke zargin gwamnatin tarayya na jagorantar sulhu da yan bindiga a jihar ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Gwamna Dauda Lawan na jihar ne ya bayyana zargin na shatale kokarin da gwamnatin jihar na magance matsalar a cikin jihar, inda yayi zargin cewa ta bayan gida gwamnatin tarayya na kokarin rattaba wata yarjejeniya da yan bindigar ba tare da saninsu ba.  A wata sanarwa da kakakin gwamnan Sulaiman Idris ya sanyawa hannu, gwamnan yace yana zargin wata tawaga daga wasu hakumomin gwamnatin tarayya na ganawa da yan bindigar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: