Sakamakon zabukan da ya gabata na kara sanya shakku ga INEC kan gudanar da sahihin zabe

0 142

Sakamakon zabukan da ya gabata, da kuma kararrakin zabe da aka shigar a gaban kotu, wanda ba a taba yin irinsa ba, ya kara sanya shakku ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci.

A zaben bana, 2023, an gudanar da zabe a kujerun siyasa daban-daban har dubu 1,280 tun daga kan kujerar shugaban kasa, da ‘yan majalisar dattijai 109, da majalisar wakilai ta tarayya 360, da kuma kujeru 782 na majalisar wakilai a fadin jihohi 28 da kuma kujerun gwamnoni 28.

Cikin jimillar adadin, an shigar da kararraki dubu 1,209 a gaban alkalai domin yanke hukunci, kamar yadda shugabar kotun daukaka kara (PCA), Mai shari’a Monica Dongban-mensem ta bayyana, a lokacin bikin fara shekarar shari’a ta 2023/2024 a Abuja.

Wannan ya nuna cewa, kashi 94.453 cikin 100 na kujerun da aka fafata, suna gaban alkalai, inda kumanin Kujeru 71 ne kacal cikin dubu 1,280 da aka fafata a zaben ba a garzaya da su gaban kotu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: