Harin babban asibitin Zirin Gaza ya fusata kungiyoyin kasa da kasa, da al’ummar sassan duniya

0 219

Harin da ya kashe mutane akalla 500 a babban asibitin Zirin Gaza, ya fusata kasashe, hukumomi, kungiyoyin kasa da kasa, da sauran al’umma a sassan duniya, wadanda ke ci gaba da yin Allah wadai da farmakin na Isra’ila.

Tuni dai shugabannin kasashen Larabawan yankin Gabas ta Tsakiya da suka hada da na Masar da Jordan da kuma na yankin Falasdinu, suka soke ganawar da aka tsara za su yi da takwaransu na Amurka Joe Biden a Laraba, biyo bayan halaka mutane 500 da Isra’ila ta yi a harin da ta kai kan wani asibitin Al Ahli inda mutane ke samun mafaka a Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta yankin Gaza ta ce akalla mutane 500 suka mutu, akasarinsu mata da kananan yara, a harin da aka kai wa asibitin Al Ahli Arab da ke kudancin Zirin Gaza.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da yayi Allah wadai da harin, ya yi kira da a tsagaita bude wuta domin bayar da damar ayyukan agajin gaggawa.

Yayin mayar da martani kan lamarin, shugaban Kungiyar Kasashen Afirka AU Moussa Faki Mahamat ya zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki musamman kan farmakin da ta kai kan babban asibitin Gaza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: