Majalisar dattijai ta yi watsi da wani kudiri na neman sake bude iyakokin Najeriya da Nijar

0 227

A jiya ne majalisar dattijai ta yi watsi da nazarin wani kudiri na neman sake bude iyakokin Najeriya da Nijar.

A watan Agusta ne gwamnatin tarayya ta rufe dukkan iyakokinta na kasa da jamhuriyar Nijar a wani bangare na takunkumin da ta kakaba wa gwamnatin mulkin sojan Nijar, wanda ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

Sanata Suleiman Kawu Sumaila, a cikin wani kuduri da ya gabatar yayin zaman majalisar na jiya, ya ce rufe iyakokin ya tabarbare harkokin tattalin arziki a garuruwa da dama a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa, Yobe da Borno.

A cewarsa, rufe iyakokin ya saba wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa da ke tabbatar da tsaro da jin dadin jama’a.

Don haka ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba batun sake bude iyakokin Najeriya da Nijar domin ba da damar zirga-zirgar kayayyaki tsakanin kasashen biyu.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce majalisar dattawan ta yanke shawarar marawa kudurorin ECOWAS baya kan al’amuran siyasa a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar ECOWAS ta sanar da kakaba takunkumai da dama kamar ‘yankin hana zirga-zirgar jiragen sama a Nijar da kuma rufe iyakokinta nan take domin tilasta wa gwamnatin mulkin sojan kasar mika mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: