Gwamnatin tarayya ta nemi gwamnatocin jihohi su bada kadada 50 domin gina gidaje ga yan kasa

0 146

Ministan gidaje da raya karka Ahmed Dangiwa ne ya yi wannan kiran a lokacin da gwamnan jihar Taraba Dr Agbu Kefas ya kai masa ziyarar ban girma jiya a Abuja.

Ya ce shirin gwamnati mai ci na sabunta gidaje yana bukatar goyon bayan jihohi wajen samar da filaye.

Dangiwa ya ce a kashin farko na aikin gwamnati ta yi shirin gina gidaje 34,500 a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa gidaje masu inganci, da rahusa ga daukacin ‘yan Najeriya shine babban abin da gwamnati ta sa gaba, inda ya kara da cewa ma’aikatar tana aiki tare da hukumar kidaya ta kasa NPC, domin tabbatar da ainihin gibin gidaje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: