An gano mutane 15,060 da ake zargin sun kamu da cutar Mashako a Najeriya

0 161

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce an gano mutane 15,060 da ake zargin sun kamu da cutar Mashako a kasar a daidai lokacin da ta ke bayar da karin haske kan matakin da kasar ke dauka kan bullar cutar Mashako da ta sake bulla kai a kasar.

Darakta Janar na hukumar NCDC, Dokta Ifedayo Adetifa, ne ya bayyana haka a taron tattaunawa na kasa da kasa na cutar Mashako jiya a Abuja.

Ya ce an samu rahoton mutane 15,060 da ake zargin sun kamu da cutar ta Mashako inda mutane 9,478 aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kananan hukumomi 137 a jihohi 20 ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Jihar Kano ce ke kan gaba a yawan masu dauke da cutar inda take da mutane 7,747, sai Jihar Yobe mai mutane 841.

Ya ce bayanan sun kuma nuna cewa kashi 71.5 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kasance tsakanin shekara 1 zuwa 14, inda jarirai suke da kasa da kashi daya cikin dari.

Haka kuma yace jihohin Kaduna, Bauchi, Borno, Katsina, Jigawa, da Yobe sun yi wa daruruwan yara allurar rigakafi ta hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: