Gwamnatin Borno ta yi rabon tallafin da yakai Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000

0 191

A jiya Alhamis Gwamna jihar Borno Babagana Zulum ya jagoranci rabon tallafi ciki har da abinci da saura kayayyaki na Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000 a Karamar Hukumar Konduga da ke Jihar.

Rabon wanda aka gudanar a cibiyoyi uku, an yi shi ne domin rage radadin da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi a watan Mayun 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa, wadanda suka ci moriyar tallafin sun hada da magidanta maza 15,000, inda kowannen su ya karbi buhun shinkafa mai nauyi kilo 25 da buhun wake kilo 10, da kuma mata 25,000 aka bai wa kowannensu kudi naira 5,000 da turmin atamfa guda-guda.

A cewar Gwamna Zulum, wannan wani yunkuri ne a kokarin da gwamnati ke yi na ci gaba da rarraba kayan tallafi ga masu karamin karfi a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: