Kungiyar kwadago ta kasa ta yi barazanar rufe aikin ta a kasar nan na tsawon wata guda

0 146

A jiya ne kungiyar kwadago ta kasa ta yi barazanar rufe aikin ta a kasar na tsawon wata guda domin nuna adawa da shirin majalisar dokokin kasar na kayyade mafi karancin albashi na kasar.

Barazanar ta NLC ta zo ne a daidai lokacin da al’ummar kasar ke jiran sabon mafi karancin albashin ma’aikata biyo bayan tattaunawar watannin da aka shafe ana yi tsakanin kungiyoyin kwadago, gwamnatin tarayya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana matsayin kungiyar a lokacin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na kungiyar ma’aikatan kasar karo na 67 a Legas.

A halin da ake ciki, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Mista Kingsley Chinda, ya ce akwai wata shawara a gaban kwamitocin majalisar dokokin kasar kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar na mayar da mafi karancin albashi daga jerin kebantattun ma’aikata zuwa jerin ‘yan majalisar dokoki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: