Sakataran kungiyar masu magani Pharmacist Kim Bot wanda aka sace ya shaki iskar yanci

0 157

Sakataran kungiyar masu magani ta kasa reshen Jihar Filato Pharmacist Kim Bot, wanda aka sace ranar Laraba ya shaki iskar yanci.

Pharmacist Kim Bot,an sace shi ne ranar Laraba da daddare a kanyar Lamingo a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Iyalan sa sun tabbatar da sakin sa ga manema labarai.

Guda daga cikin yan uwan sa yace an saki Pharmacist Kim Bot duk da cewa da farko yan bindigar sun nemi kudin sa da bai bayyana adadin sa ba.

Majiyoyi daga Iyalan sa sunce an kai shi Asibiti inda yake cigaba da karbar magani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: