An kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane 2 da kuma yan ta’adda 89 a Kaduna

0 289

Dakarun sojoji na musamman a Jihar Filato sunce jami’an su sun kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane 2 da kuma yan ta’adda 89 a jihar da kuma Kaduna mai kwabtaka da ita.

Jami’an yada labarai na rundunar a jihar Filato Kaftin Oya James shine ya bayyana haka jiya a Jos babban birnin jihar.

James yace dakarun sun gudanar da ayyuka a wurare mabanbanta cikin makonni 2 kuma sun samu nasara.

Ya kuma kara da cewa dakarun sun samu nasarar kama wasu mutane 4 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kubutar mutane masu yawa da aka garkuwa da su, da kwato shanun sata.

Wadanda ake zargin suna da hannu a sace dalibai 7 na jami’ar jihar Filato da a ka yi watan Yulin wanna shekarar.

Jami’an sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 da alburusai a hannun bata garin. Kwamandan dakarun ya tabbatar da cewa za’a gurfanar da wadanda ake zargin a gab kotu da zarar sun kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: