Radadin faduwa zabe ne yasa Atiku ke neman a soke nasarar Bola Tinubu – Felix Morka

0 255

Jam’iyyar APC tayi ikirarin cewa dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar,radadin faduwa zabe da yayi a zabuka daban-daban ne yasa neman soke nasarar shugaba Tinubu.

Alh Atiku Abubakar wanda ya fadi zabe a shekarar 2023 da kuma 2019, ya yiwa manema labarai jawabi bayan da jami’ar Jihar Chicago ta kasar Amurka ta fitar da shedar takardun karatun shugaban kasa Bola Ahmed, wanda tunda da farko yayi zargin cewa shugaban kasa ya gabatar da takardun bogi yayin tsaya takarar shugabanci kasa a wanann kasar.

Sai dai mai magana da yawun jami’iyyar APC Felix Morka ya karya ta jawabi Atiku Abubakar. A cewar sa, Atiku da tawagar sa ya kamata su janye shigar da kara kan nasarar shugaba Tinubu da kuma kalubalantar gabatar da takardun bogi na jami’ar Jihar Chicago dake kasar Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: