Majalisar Dattawa ta nuna damuwa dangane da matsalar tsaro a kasar nan

0 165

Yan majalisar sun bayyana cewa samar da yan sanda Jihohi shine kadai hanya dala tilo da zata magance matsalar.

Dattawan kasar nan sun fadi haka ne yayin da suka kira manyan Hafsoshin tsaron kasar nan domin suyi jawabi a gaban majalisar dangane da yadda zasu magance matsalar tsaro a kasar nan, da kuma bukatar jami’an tsaro su dauki mataki kan Yan bindiga, masu garkuwa da sauran masu tada kayar baya, musamman a yankin arewa maso gabas da arewa maso yammcin Kasar nan.

Matakin na majalisar Dattawan na zuwa ne bayan amincewa da kudirin da Sanata Abdulaziz Yar’Adua ya gabatar a zaman majalisar na jiya.

Da yake gabatar da kudurin,Sanata Yar’adua ya nuna damuwa dangane da sace dalibai mata 5 na jima’ar gwamnatin tarayya dake Dutsin-Ma ta jihar Jihar Katsina a dakunan kwanan su ranar laraba.

Yace yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na karuwa sosai a manyan biranen kasar nan musamman a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.

Dan majalisar Dattawan ya bayyana bukatar kirkir yan sandan jihohi a matsayin wata hanya daya tilo data magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: