Jam’iyyun adawa 11 a Kasar Zambiya sun kalubalanci matsin tattalin arziki dake karuwa a kasar

0 184

Gamayyar jam’iyyun adawa 11 a Kasar Zambiya sunyi wata hadin giwa domin kalubalantar matsin tattalin arziki, talauci da fatara da kuma rashin aikin yi da suka ce ya karu a gwamnatin shugaba Hakainde Hichilema na kasar.

Shugabannin jam’iyyun, wanda suka gabatar da taron manema labarai a jiya, sunce sunyi matukar damuwa tare da kira ga babban zauren kasar domin tattauna matsalolin da kuma hanyoyin magance su.

A wata wasika da suka aikewa shugaba Hakainde, sun bayyana abubuwa 8, daga ciki har da karuwar farashin kayayyaki, rashin aikin yi da kuma cin zarafin yan adawa.

Jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi ta kasa APCP da kuma tsuhuwar jam’iyya mai ci ta yan ra’ayin rikau na daga cikin wadanda suka rattaba hannu a kan wasikar.

Kasar da ke kudancin Afirka ta fuskanci matsalar basussuka na tsawon shekaru uku, ta zama kasa ta farko a Afirka da ta gaza biyan basussukan da ta ke bi a lokacin barkewar cutar ta Corona. A watan Yuni ne dai shugaba Hichilema ya gabatar da tsarin yarjejeniyar da aka kulla da nufin fitar da kasar Zambiya daga cikin ja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: